Saba wa iyaye
Tambaya
Mene ne sakamakon saba wa iyaye?
Amsa
Allah madaukakin Sarki ya hana sava wa iyaye, ya kuma tanadar da sakamako mai muni ga duk wanda yake yin haka; akwai sakamakon da tun a duniya zai faru kafin kuma a tafi lahira; an ruwaito Hadisi daga Anas Bn Malik (Allah ya kara yarda da shi), cewa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Zunubai guda biyu tun a duniya ake yin ukuba akansu: zalunci da saba wa iyaye) [al- Hakim].
Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya lissafa saba wa iyaye a matsayin abin da yake hana shiga aljanna, an ruwaito Hadisi daga Ibn Umar (Allah ya kara yarda da su) Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Mutane guda uku, Allah mai girma da buwaya ba zai kale sub a a ranar alkiyama: mai saba wa iyayensa, da macen da ta mayar da kanta namiji, da namiji mara kishin matarsa. Kuma mutane uku ba za su shiga aljanna ba: mai saba wa iyayensa, da mashayin giya, da mai gori akan kyautar da ya yi) [an- Nasa'i].