Yunƙurin dawo da halifancin da ake riyawa
Tambaya
Mene ne hukuncin yunƙurin dawo da halifancin da ake riyawa?
Amsa
A cikin abubuwan da suke ƙunshe a cikin manufofin shari’a a dunƙule, akwai bayanin cewa: duk irin yanda sunayen abubuwa suka sauya a wasu lokuta, to abin lura a ciki shi ne: shi abin da aka yi wa sunan, da abin da zai tabbatar da maslahar mutane a rayuwarsu ta duniya, ya kuma tabbatar masu da tsaro, kuma duk wani yunƙuri na samar da abin da yake samamme ne shi, to kuwa lallai hakan wasa ne da ɓata lokaci, saboda haka yunƙurin dawo da halifancin da ake riyawa wasa ne da ɓata lokaci, ita kalmar halifanci a duk sanda aka ambace ta tana ɗauke ne da ma’anoni da dama, ya halatta ka kira kowane mutum da sunan Halifa, Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: (Lallai ni zan sanya halifa a doron ƙasa) [al- Baƙra: 30], saboda kowane mutum yana halifantar waninsa, halifar Musulmai kuma shi ne: shugabansu gaba ɗaya, saɓanin minista da gwamna, an kuma kira shi da wannan suna ne saboda yana halifantar wanda ya gabace shi a shugabanci, ba sharaɗi ne sai ya zama shugaban dukan Musulmai ba sannan wannan suna ya tabbata akansa, lallai an yi halifofi masu yawa a zamani guda ɗaya a cikin tarihi, inda aka sami daular Abbasiyyawa a gabashin duniya, a daidai lokacin da akwai daular Umawiyyawa a Andalus (Spain), saboda haka kiran kowane shugaban Musulmai da ya zo, ko zai zo a bayansu da sunan halifa abu ne da ya halatta; saboda ya halifanci wanda ya gabace shi ne.