kokarin da Hukumar bayar da fatawa ta kasar Misra take yi wajen yakar tsattsauran ra’ayi da Ta’addanci
Tambaya
Mene ne ƙoƙarin da Hukumar bayar da fatawa ta ƙasar Misra take yi wajen yaƙar tsattsauran ra’ayi da Ta’addanci?
Amsa
Hukumar bayar da fatawa ta ƙasar Misra Cibiya ce ta ƙasa mai girma, tana bin tsarin ilimi na tsaka-tsaki, mai rangwame wanda yake bayyana haƙiƙanin Addinin Musulunci, a bisa haka ne ya sa tun nesa da ƙofa hukumar ta lura da hatsaarin ƙungiyoyin masu tsaurin ra’ayi, sannan ta yi gaggawar tunkarar irin wancan lalatattun tunani tare da fatawowi na daban a cikin wannan addini namu na ƙwarai. Ya kasance daga cikin muhimman manufofin (Sateriyar hukumomi da cibiyoyin bayar da fatawa ta duniya) da hukumar bayar da fatawa ta ƙasar Misra ta taka rawa sosai wurin ƙirƙiro ta, akwai: yaƙi da tunani gami da fahimtar masu tsattsauran ra’ayi, tare da tabbatar da manhajin tsaka tsaki, haka nan hukumar bayar da fatawar ta ƙasar Misra ta samar da (Mimbari da yake zama Madakatar fatawar kafirtawa tare da tsattsauran ra’ayuyyuka), daga cikin ayyukan wannan sashe akwai bibiyan kalaman kafirtawa da ake yaɗawa a kafafen yaɗa labarai na zamani, wanda ake karantawa, ko ake sauraro, ko ake kallo, tare da bayar da cikakken goyon baya ga cibiyar bayar da fatawa wurin datse bakin waɗancan ƙungiyoyin, haka nan yana daga cikin ƙoƙarin hukumar bayar da fatawar samar da (Cibiyar Salam mai nazarin akan tsattsauran ra’ayi), ta hanyar waɗannan hukumomi da cibiyoyi da saurasu ne, hukumar bayar da fatawa ta ƙasar Misra take kaiwa da komowa kan lamuran da suke faruwa a yanzu ta ɓangarori da daman gaske, kamar ta hnayar ilimi da tunani domin gabatar da abu mafi dacewa a wannan sashe ga ɗaukacin mutane baki ɗaya a faɗin duniya.