Matsayar magabata nagari akan Hawar...

Egypt's Dar Al-Ifta

Matsayar magabata nagari akan Hawarijawa

Tambaya

Mene ne matsayar magabata nagari akan Hawarijawa?

Amsa

Magabata nagartattu musamman sahabban Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) sun yi mu’amala da Hawarijawa ta fuskar yin tsayin daka wajen hana su yin gaba- gaɗinsu, tun daga farkon bayyanarsu na zahiri, sun kasance kamar wata ƙungiya ce ta Musulunci a zamanin halifancin Imam Aliyu Bn Abuɗalib (Allah ya ƙara yarda da shi), a farko ya aika masu da Abdullahi Bn Abbas, domin ya bayyana masu irin ɓatar da suke ciki, ya kuma ba su amsar matsalolin da suka tsinci kansu a ciki waɗanda suka kai su ga faɗawa cikin halaka, sakamakon haka ne kashi ɗaya bisa ukunsu suka dawo daga rakiyar wannan tunani nasu mai muni, yayinda sauran kuma suka tsaya cikin ɓatarsu da ficewa daga layin shiryayyu, sai Imam Aliyu ya yaƙe su a matsayinsa na shugaban Musulmai a lokacin, hakan ya yi daidai da wasiyar da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yi na cewa: (Su ne mafi sharrin mutane da sauran halittu, madallah da wanda ya kashe su, ko suka kashe shi a tafarkin Allah, domin suna kira ne zuwa ga littafin Allah, amma ba su daga cikin masu binsa da komai, duk wanda ya yaƙe su, to shi ne mai daraja a wurin Allah a ba su ba..) [Abu Dawud], amma fa duk da hakan babu wani lafazi bayyananne daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), ko daga sahabbai da yake nuni akan kafircinsu, da fitarsu daga Musulunci.

Share this:

Related Fatwas