Laifuffukan da ƙungiyar ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da BH..) suka aikata
Tambaya
Mene ne laifuffukan da ƙungiyar ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da BH..) suka aikatawa?
Amsa
Ƙungiyar ‘yan ta’adda ta ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da BH..) sun aikata laifuffuka masu yawa da Shari’a ta hana, wannan kuwa duk da cewa waɗannan ƙungiyoyi na mashaya jinni sun kafu ne wai domin su aiwatar da Shari’ar Musulunci, da suke riya cewa wai ba a aiki da ita, a cikin waɗannan laifuffuka akwai: tirsasa wa waɗanda ba Musulmai ba su shiga Musulunci daidai da mummunan i’itiƙadinsu, da ɓataccen manhajinsu, ko kuma su biya jiziya, haka ma suna amfani da azabtarwa da tsoratarwa da kisa domin tirsasa wa mutane su yi wa halifansu mubaya’a, da kuma yawaita kisa da fajirci da yin alfahari da haka, su kuma ɗauki hoton bidiyo na wannan munanan ayyuka su yaɗa a intanet, kuma lallai Shari’ar Musulunci ta hana aikata haka, haka ma suna hana karantar da tirihi, da Adabin ƙasa, wanda yake ɗauke da al’adu, ko addinan da suka saɓa da manhajinsu, haka ma sun ɗauki tuta baƙi a matsayin takensu, kuma suna riya cewa hakan shi ne Sunna, bayan cewa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) bai ɗauki wani launi guda ɗaya domin ya zama masa tuta ba, haka ma suna hana mutane shiga tsangayoyin aikin soja da ‘yan sanda, wai saboda kada wanda ya shiga ya zama ya taimaki shugabanni da suke adawa da su, haka ma sun haramta yin karatu a tsangayoyin dokoki, wai saboda karantar dokokin zamani ya saɓa da shari’a kaman yanda suke riyawa!