Mummunar tarbiyya da ganin fifiko da girman kai da ruɗi suke manyan ƙofofin amsar fahimtar masu tsattsauran ra’ayi
Tambaya
Saboda mene ne ake ɗaukan mummunar tarbiyya, da ganin fifiko, da girman kai, da ruɗi a matsayin manyan ƙofofin amsar fahimtar masu tsattsauran ra’ayi? Kuma mene ne maganin haka?
Amsa
Babu shakka cewa yi wa halittar Allah girman kai ɗaya ne daga cikin munanan ɗabi’un da shari’ar Musulunci ta zarga, ayoyin Alƙur’ani da Hadisan Annabi masu dama ne suka bayyana haka, kuma duk da haka girman kai ɗaya ne daga cikin sifofin da suke fi fice a tare da dukan masu tsauraran ra’ayi, domin ƙa’idojinsu irinsu: ɗaga kai saboda imani, da jahiliyyar al’umma, da ƙaurace wa tunanin al’umma, duka ƙa’idoji ne da zukatan masu girman kai suke yi na’am da su, suna kuma samun cikakkiyar natsuwa a tare da su, babu wani bambanci na a zo a gani tsakanin mutumin da yake yi wa halittar Allah girman kai saboda ya sami duniya, ya tara dukiya da matsayi, da mutumin da yake yi masu girman kai saboda yana aikata ayyukan addini irin su zikiri da sallah da sauransu, duka dai a ƙarshe sakamakon ɗaya ne, abu ma fi wahala ga zuciyar mai girman kai shi ne ya zama yana da tawali’u, ko ya ƙudiri aniyar cewa dukan mutane suna da alhairi, kada ya rinƙa yi masu mummunan zato. Lallai kowa ya san cewa girman kai zunubi ne babba, wanda shi ne ma ya yi sanadiyyar da aka fitar da shaiɗan daga gidan aljanna, lokacin da ya ji cewa yana da fifiko akan Annabi Adam (AlaiHis Salam), ya ƙi ya yi masa sujada kaman yanda Allah mai girma da buwaya ya bayar da umurni, saboda haka ne malaman tarbiyya cikin malaman Musulunci suka duƙufa wajen ɗaura almajiransu akan ɗabi’ar tawali’u, da sauƙin kai.