Ingantaccen Sufancin Musulunci

Egypt's Dar Al-Ifta

Ingantaccen Sufancin Musulunci

Tambaya

Wasu mutane suna riya cewa: wai lokacin Sufanci na gaskiya ya riga ya wuce, a wannan zamanin babu ingantaccen Sufanci na gaskiya, shin wannan maganar haka take? 

Amsa

Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana cewa: (Ba za a taɓa rasa jama’a da za su tsaya tsayin daka wajen zartar da al’amarin Allah a cikin al’umma ta ba, wanda ya bayar da su, ko ya saɓa masu ba zai taɓa tasiri akansu ba, har zuwa lokacin da al’amarin Allah zai kasance..) [al- Bukhari da Muslim], haka ma (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana cewa: (Al’ummata kaman ruwan sama suke, ba a sanin farkonsa ne alhairi ko ƙarshensa) [al- Mu’ujamul Ausaɗ]; saboda haka, alhairi yana cikin al’ummar Musulmai har zuwa ranar alƙiyama, Sufanci a yanzu wani jeri ne cikin jeri mai tsawo, wanda ya fara daga Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), ya biyo da wurin Sahabbai masu girma, zuwa ga shugabannin tabi’ai, zuwa har Imamuɗ Ɗa’ifa al- Junaid, da Hujjatul Islam al- Ghazaliy, da fitaccen Tauraron nan Sayyidiy Abdulƙƙadir al- Jailaniy, da waɗanda suka biyo bayansu irinsu Sayyidiy Abul Hassan al- Shaziliy, da almajirinsa Sayyidiy Abul Abba sal- Mursiy, har zuwa wannan zamani da muke ciki, kai har zuwa lokacin da Allah zai gaje doron ƙasa da abubuwan da suke akanta, shi kuwa samun kura- kurai da kauce hanya wannan abu ne sananne, da yake bijiro wa duk wani ƙoƙarin da ɗan Adam yake yi, zai yiwu a same su a wannan zamanin kaman yanda aka same su a jiya, abin da ya wajaba game da shi ne magance su, da sake daidaita su akan hanya, ba wai riya cewa wai zamanin Sufanci ya riga ya wuce, ko wata magana mai kama da wannan ba.

Share this:

Related Fatwas