Taruwa saboda a yi wa mamaci addu’a
Tambaya
Mene ne hukunci taruwa don a yi wa mamaci addu’a a kabarinsa?
Amsa
Sunna ne masu raka jana’iza su tsaya a kabari na dan wani lokaci bayan sun rufe shi su yi masa addu’a, babu laifi su yi masa talkini.
Shi wannan addu’a ko zikiri da ake yi wa mamaci, za a iya yi a sirri ko a bayyane, da kuma kowace irin siga; abu ne mai yalwa, an fi fatan amsar addu’ar da jama’a suka yi a tare, kuma haka ya fi farkar da zukata, da tattara himma a wuri daya, da kuma nuna kankantar da kai a gaban Allah Madaukakin Sarki.