Ma’anar samun madafan iko (Attamkin)
Tambaya
Mene ne ma’anar kalmar samun madafun iko (Attamkin) a cikin Alkur’ani da Hadisai, kuma ta yaya kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi suka sauya wannan ma’anar?a
Amsa
Ma’anar samun madafun iko (Attamkin) a cikin Alkur’ani da Hadisai tana jujjuyawa ne akan ma’anoni masu dama, da suke nuni zuwa ga yawan manufofin da suke tattare da haka; kaman samun daman da Allah yake bai wa muminai wajen tabbatar da addini, wannan shi ne karshe, ko kololuwar manufa ta samun tamkini, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: (Su ne wadanda idan muka ba su dama a bayan kasa za su tsayar da sallah, su kuma bayar da zakka, su bayar da umurni da kyawawan ayyuka, su kuma hana aikata munanan ayyuka) [al- Hajji: 41], ko hore wa bani Adama doron kasa, kaman yanda ya zo a inda yake cewa: (Lallai mun riga mun ba ku cikakken dama a bayan kasa, muka kuma sanyata ta zama maku wurin rayuwa, kadan daga cikin mutane ne suke godewa) [al- A’araf: 10], ko bayar da mulki da dama, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: (Lallai mun ba shi cikakken dama a doron kasa, sannan kuma mun ba shi sababin komai) [al- Kahfi: 84], a takaice: lallai ma’anar kalmar (Attamkin) ma’ana ce mai fadi, ta zo ne domin nuna cikakken ikon Allah, da kuma irin yanda yake tabbatar da bayinsa ya mallaka masu abin da duk ya ga dama, ma’ana Allah dai shi ne mai bayar da wannan dama da karfinsa da dubararsa, shi ya sanya ya jingina tabbatarwar zuwa ga zatinsa mai girma da daukaka, wannan ita ce ingantacciyar ma’anar (Attamkin), wato yana zuwa ne daga Allah mai girma, sai dai duk da haka, sai da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi suke takaita ma’anar (Attamkin) da kungiyoyinsu kadai, inda suka nufi haka ce cewa shi ne darewa a madafun iko na shugabanci da siyasa, da zartar da wannan tamkini da karfinsu gami da ikonsu, ba wai ta tabbatarwa daga Allah ba, da haka sai suke sace ma’anar Tamkini, suke lankwaya ma’anarta ta yadda za ta yi daidai da manhajinsu, da mafuskantarsu ta siyasa, suka kuma gurbata mata ma’ana.