Kafirtawa hukunci ne na kotu
Tambaya
Mene ne dalilin da ya sanya kafirtawa ta zama aiki ne na alkali a kotu?
Amsa
Kafirtawa hukunci ne na shari’a a kotu; saboda daukan hukuncin kafirtawa yana tattare da daukan wasu matakai da suke da dangantaka da dukiyoyi, da kare jini, da kiyaye hakkoki, da alfarmar Musulunci, saboda haka, yin haka ba abu ne masauki ba, hasali ma babban abu ne mai cike da fitina da take barazana ga tsaron mutane da daukacin al’umma, sannan kuma ganin cewa kungiyoyin da ba hukumomin shari’a ba, ba su da kwarewar daukan matakan tabbatuwar sharuddan kafirci ko rasa su, ko ma rashin ingancinsu, ganin cewa su din ba hukumomi ne na bincike ba, ba kuma su da gwanancewar da za ta ba su daman shiga cikin wannan al’amari mai matukar hatsari; saboda haka, hukumomin shari’a ne kawai aka ba su wannan aiki, ganin cewa shi alkali wakili ne na al’umma, saboda haka wajibinsa ne ya gabatar da wannan aiki wajen kare rayuka da kiyaye hakkoki, da suke kai wa zuwa ga kiyaye rayuwar zamantakewar al’umma daga ‘yan a fasa kowa ya rasa, da barnar mabarnata, da suke tafka barna a bayan kasa ba tare da wani dalili ba, yin haka ne zai kiyaye al’umma daga zarmiyen wasanni da rashin tsari da rudani, da rarrabuwar kawuna.