Nau’ukan tsattsauran ra’ayi.

Egypt's Dar Al-Ifta

Nau’ukan tsattsauran ra’ayi.

Tambaya

Wani abu ne ake kira da tsattsauran ra’ayi mai zafi, kuma ta yaya za mu fahimce shi?

Amsa

Tsattsauran ra’ayi mai zafi shi ne abu mafi girma a dandamalin kololuwar tsattsauran ra’ayi, a lokacin gudanar da ayyukan da suka shafi tsattsauran ra’ayi mai zafi wadansu tunanunnuka su kan bayyana da nazarurruka da fatawowi da suke haifar da aikata munanan ayyuka da ‘yan ta’adda ke aiwatarwa domin cimma muradunsu.

Don haka shi Tsattsauran ra’ayi mai zafi yana kasancewa ne sakamakon cigaba da gudanar da ayyukan masu tsauri wacce ba ta dakatawa ko natsawa sakamakon yanda yanayin lamaura suke cancanzawa, tare da samun sauyi mai yawa a tsarin rayuwar daidaikunsu ko jama’arsu, wanda hakan ke farlanta kansa a bisa wancan zangon da suke ciki, hakanan kwarewar da suke da shi na zamansu a karkashin wannan ra’ayi na su mai tsauri.

Yana daga cikin abubuwa masu muhimmanci da ya kamata a lura da su anan wato dai wannan matakin ba wai mataki ne da ke iya lizimtar wasu matakai na daban ba, ai ma wannan matakin na zama mafi kololuwan matakai na zafafawa, wanda hakan zai iya kai mutum zuwa ga matakin karshe na tsauri kai tsaye ba tare da shamaki ba, hakanan lamarin na iya kaiwa ga mutum ya shiga sahun wadanda ake baiwa horon zama mai tsattsauran ra’ayi a hankali, wanda hakan zai kai ga wanke tunaninsa na asali zuwa koya masa na tsattsauran ra’ayi.

Saboda haka tsattsauran ra’ayi mai zafi ba wai yana da wata hanya ta koyo bace ta musamman, saboda aikace aikacen ta’addanci su na iya tasowa sakamakon korafi ko zanga zanga na wasu mutane ko na siyasa, kai har ma da tarzoma na nuna kiyayya ga wani abu da ake yi ba tare da wani tsararren shiri ba,  saboda haka shi tsaurancin ra’ayi wanda ya ginu akan wata manufa ta musamman shi ma yana iya shiga cikin wannan layin, duk wani tsaro ko salon na tunani na da ikon samar da tsattsauran ra’ayi, domin haka shi tsattsauran ra’ayi mai tsari wani tsagi ne na ta’addanci, domin shi ma ya shafi wani abu ne wanda ke iya faruwa ba tare da wani tsari ko fahimta ba.

Share this:

Related Fatwas