Abubuwan da su ke ingiza mai tsatts...

Egypt's Dar Al-Ifta

Abubuwan da su ke ingiza mai tsattsauran ra’ayi aikata laifukansa (3)

Tambaya

Mene ne tasirin kebantaccen tunani da jirkicewar kwakwalwa a wurin mutum mai tsattsauran ra’ayi?

Amsa

Lallai mutumin da ya siffantu da tunani makadaici baya iya fuskantar matsin lambar matsalolin da yake fuskanta, saboda bai da wasu hanyoyin da zai iya kare kansa ta hanyoyin da suka dace,  a koda yaushe tuninsa mai cin karo da juna ne, sam ba shi da sassauci akan lamura, kullum yana cikin rudani kan samun nasara ko rashin nasara akan lamuran da suka shafi rayuwansa, ko dai ya kasance mai soyuwa ga al’ummansa ko kuma wanda sam ba a damu da shi ba, haka dai rayuwarsa take kullum, hakan yakan kai mutum zuwa ga rungumar ra’ayin ta’addanci, daga nan kuma sai ya fada cikin kungiyoyi na ‘yan ta’adda saboda su wandacan kungiyoyin suna da abin da ya rasa a wurin al’ummar da yake rayuwa a cikinsu, sai kungiyoyin su kasance masa mafaka da kuma wurin samun natsuwa, domin kuwa ba inda zai samu wannan kwanciyar hankalin idan ba wurinsu ba.

Amma motsawar kwakwalwa wani rashin lafiya ne da yake samun wasu mutane, ta yanda mai fama da wannan lalurar zai rinka jin cewa babu wani mutum nagari mai tsarkake aikinsa kuma jagora mai girma kamarsa a cikin al’umma, wanda hakan ke kai shi ga aikata munanan ayyuka a duk sanda ya kara sakaye abinna yake cinsa a zuciya, hakan yana karfafa tsattsauran ra’ayin zance ya koma aikata munanan ayyuka a cikin al’ummarsa.

Share this:

Related Fatwas