Abubuwan da su ke ingiza mai tsattsauran ra’ayi aikata laifukansa (4)
Tambaya
Mene ne tasirin ingiza kai, da son rai ga mutum mai tsattsauran ra’ayi?
Amsa
Ingiza mai kantu ruwa anan dai shi ne tsanantawa akan komai da komai, shin wannan tsanantawar ta kasance na nuna soyayya ne ko nuna kiyayya ko kuma fushi, mutum mai halayyar saurin tunzura ba ya iya daukan tsaka tsaki a dukan lamura na rayuwa, hakanan tunaninsa akan mutane duk irin haka ne, saboda haka akan iya samun wanda tsananin soyayya zai iya tunkuda shi zuwa ga shiga sahun ‘yan ta’adda kawai saboda acikinsu akwai wanda yake tsananin so, sai ya karkata zuwa garesu tare da aikata abubuwan da suke aikatawa kawai saboda akwai wanda yake so a cikinsu, amma akasin haka shi ne mutum ya nuna kiyayyansa ga wani ko wasu mutane na musamman wanda hakan zai iya kai shi ga amanna da shiga sahun masu ra’ayi ko kungiyar ta’addanci wanda shi wannan mutumin ko kuma saboda abin da mutanen suke aikatawa, hakanan kuma rashin tabbaci akan abin da mutum yake iya ji a jikinsa da kuma matsa kaimi wurin mayar da martini zai iya jefa mutum cikin layin ‘yan ta’adda.
Amma karkata zuwa ga son kebancewa daga cikin al’umma da yawan masu nazari suna kallon mutumin da yake da ra’ayin ta’addanci a matsayin mai son warewa wuri daya baya son shiga cikin mutane, domin kuwa alaka tsakanin kebancewa da ta’addanci wani abune da yake komawa zuwa ga yanda ‘yan ta’adda su ke yawan yin bayani akan alfanun warewa da zaman kadaici, wannan yanayin shi ne yake sanya mai wannan ra’ayin jin sauki sosai wurin karkata zuwa ga wadanda suke da ra’ayi ko fahimta irin daya da na sa, inda a karshe masu irin wannan halin ke kasancewa a sahun gaba wurin yin mafani da su a ayyukan ta’addanci fiye da wasu da ba su da irin wannan ra’ayin ko tunanin tun farko.