Sharuddan gabatar da fatawa

Egypt's Dar Al-Ifta

Sharuddan gabatar da fatawa

Tambaya

Mene ne sharuddan da suke kan wanda yake bayar da fatawa a Musulunci?

Amsa

Shi bayar da fatawa bayar da labari ne akan hukunci na shari’a bisa wani abu da ya faru ko wata matsala mabayyaniya daga cikin matsaloli na rayuwa, saboda muhimmancin da yake tattare da wannan aiki, hakika malamai sun sanya wasu sharudda da ya wajaba a same su ga duk wanda yake son bayar da fatawa, ya wajaba ga mai bayar da fatawa ya kasance masani a bangaren fikihu da usulinsa, ya kasance mai fahimta ga maganganun malamana fikihu, masani kuma akan lamura da halayyar mutane, kuma mai iko wurin bambance abubuwan da suke tabbatattu da masu canzawa, kuma masani akan abubuwan da suke da muhimmanci a matakin farko da wadanda suke bukatar daidaito, da kuma sanin hanyoyin yin istinbadi, daga dalilai na shari’a.

Shi bayar da fatawa ba tare da ilimi ba haramun ne a shari’ance, saboda hakan yin karya ne ga Allah – Mai girma da daukaka– da kuma Manzonsa SallallaHu AlaiHi Wasallam da kuma batar da mutane.

Daga karshe, ya wajaba a wannan zamanin a kara wani sharadi na kwarewar ilimi da manhaji ingantacce wanda ya shafi amsar ilimin daga cibiyoyin da suke bayar da fatawa, wanda hakan ne zai mayar da mutum mufti wanda aka aminta da shi daga cibiyoyin bayar da fatawar Musulunci a duniya.

Share this:

Related Fatwas