Dangantawa Allah Ta’ala wuri

Egypt's Dar Al-Ifta

Dangantawa Allah Ta’ala wuri

Tambaya

Shin Asha’ira suna danganta wa Allah Ta’ala wuri na cewa yana ko’ina?

Amsa

Su shugabanni na Asha’ira ba sa cewa: Allah Ta’ala yana ko’ina, ai babu wani ma daga cikinsu wanda ya fadi hakan,  yana daga cikin abin da aka sani cewa su shugabannin Ash’ariyyawa su na tabbatar da korewar yiwa Allah Azza wa Jalla wuri da kuma jiha a mazahabarsu, su ai ahalin tsarkake Allah SubhanaHu wa Ta’ala ne ga zatinsa da siffofinsa, su Ahalus Sunnah wal Jama’a ne wadanda akidarsu ke zama mafi rinjaye a cikin al’umma ada da yanzu, da kuma malamansu da shahararrunsu, to wai ta yaya wani wuri zai iya dauke wanda ya samar da shi? To da hakan ya wajabta samuwarsa a wurin ko kebantuwa a wurin, Allah ya tsarkaka daga haka, tsarkaka mai girma, Abdul-Kahir Al’bagdady yana cewa: (Sun hadu akan cewa babu wani wuri da zai iya daukeshi kuma zamani baya iya riskansa), wato dai Asha’ira Kenan, wannan ita ce akidar salaf daga cikin sahabbai Allah ya yarda da su, Imam Aliyu Allah ya yarda da shi yana cewa:(Allah ya kasance ne ba a wani kebantaccen wuri ba, shi yanzu ya kasance ne a inda ya kasance), ai shi Allah SubhanaHu wa Ta’ala babu wani wuri samamme da yake iya dauke shi, matukar lamarin dai shi ne mai ruduwa zai iya rudewa kan Ash’ariyyawa suna fadin hakan cewa: Shi Allah yana zagaye da ko’ina da komai da iliminsa, babu wuri babu zamani face yana sane da shi, to wannan ba abin da suke rayawa bane a kalamansu.

Share this:

Related Fatwas