Hukuncin cakuduwa

Egypt's Dar Al-Ifta

Hukuncin cakuduwa

Tambaya

Shin cakuduwar mata da maza yakan kasance haramun ne a shari’ance baki daya, kuma ya wajaba a hana hakan a kowani wuri?

Amsa

Lallai cukuduwa tsakanin maza da mata babu hani akan hakan a shari’ance idan yakasance akwai iyaka da kuma tsari na aminci bisa gwargwadon koyarwan addinin Musulunci, kamar dai yanda yake gudana na cakuduwa tsakanin maza da mata a wuraren karatu kamar makarantu da jami’oi, da ababen hawa na bai daya, haka nan wuraren aiki da sauran wuraren na rayuwar mutane na bai daya da wuraren samun amfaninsu, matukar namiji da mace kowannensu yana kiyaye laduban Musulunci kamar shigar kamala ga mace da kame harshenta da runtse idonta akan abin da shari’a ta yi hani akansa, tare da nesantar kebancewa da juna wanda yake kai ga tozarta hurumi ko sanya shubuha, haka nan ya wajaba akan namiji ya runtse idonsa da kiyaye hurumomin Allah – Azza wa Jallah -  idan haka ya tabbata to babu laifi a shari’ance a samu cudanyar maza da mata, Allah Ta’ala yana cewa: (ka gayawa muminai su runtse idanunsu su kiyaye yin zina wannan shi ne mafi tsarkaka garesu lallai Allah masani ne da abin da suke aikatawa) [Nur:30] amma idan namiji da mace suka kasa kiyaye dokokin shari’a ta Musulunci da koyarwarsa kuma cakuduwarsu zai haifar da fitina zai iya kaiwa ga aikata laifi da haramtattun abubuwa to wannan cakudan ya haramta.  

Share this:

Related Fatwas