Yi wa mamaci addu’a a jam’i

Egypt's Dar Al-Ifta

Yi wa mamaci addu’a a jam’i

Tambaya

Mene ne hukuncin yi wa mamaci addu’a a jam’i a kabarinsa?

Amsa

Sunna ne mutanen da suka raka mamaci zuwa kushewa su tsaya na dan wani lokaci bayan rufe mamaci su yi masa addu’a, babu laifi idan sun yi masa takini, (ma’ana su rinka cewa: wane ka ce La’ilaha illalLahu Muhammadur RasululLahi).

Shi yi wa mamaci addu’a da karanta zikiri a wurin kabarinsa ana yi ne a asirce ko a bayyane, da kuma kowace irin siga da take kunshe da haka; wannan al’amari ne mai yalwa, an fi fatan amsar addu’ar da aka yi ta a cikin jama’a, ta ma fi jawo hankula ta farkar da zukata, da sanya himma da nuna kankan da ka a gaban Allah Madaukakin Sarki.

Allah shi ne masani.

 

Share this:

Related Fatwas