Salatut Tauba
Tambaya
Mene ne hukuncin salatut Tauba? Kuma yaushe ake yinta?
Amsa
An ruwaito daga Abubakar (Allah ya kara yarda da shi) ya ce: na ji Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana cewa: (Babu wani mutum da zai aikata zunubi, sannan ya tashi ya yi alwalla, ya kuma yi sallah, sannan ya nemi gafarar Allah, face an gafarta masa) sannan ya karanta wannan ayar: (Su ne wadanda idan sun aikata alfasha, ko sun zalunci kawunansu, suka tuna Allah, sai su nemi ya gafarta masu zunubansu) [Ali Imran: 135] [al- Tirmizi a cikin Sunan].
Wannan Hadisin yana nuni ne zuwa ga halaccin salatut Tauba, mustahabi ne a dukan mazhabobi guda hudu, an so duk wani Musulmi da ya aikata sabo ya yi alwalla, ya kuma kyautata yin alwallar, sannan ya yi sallah raka’a biyu, ya yi iya bakin kokarinsa wajen halarto da tsoron Allah Madaukakin Sarki, sannan ya nemi gafarar Allah, Allah mai girma kuma ya gafarta masa saboda karamcinsa. Amma dole ne ya cika sharuddan tuba, ma’ana ya yi nadama akan sabon da ya aikata, ya kuma dauri aniyar rashin sake aikatawa, idan sabon yana da jibi da hakkokin bil’adama ya mayar masu da hakkokinsu.
Allah shi ne masani.