Abin da ake nufi da Ahlul-zikr
Tambaya
Su wane ne Ahlul zikr, shin abin nufi da su malaman addini ne kawai?
Amsa
Allah Ta’ala ya ce: (Ku tambayi ma’abota sani matukar kun kasance cikin rashin sani) [An-Nahli: 43]. Abin nufi da “Ahlul zikri” anan shi ne masana kwarewa a fanni na ilimi da kwarewa cikin kowani bangaren ilimi, kuma wannan ya ginu ne akan ma’anar lafazin Ayar mai girma ba wai ma’anar da Ayar ta kebanta da shi ba, don haka aka dorawa lafazin ma’ana mai fadi domin hakan yafi dacewa matukar ba wani kebantaccen abu ne ya rataya da ita ba, don haka sai ayi tambaya ga ma’abota sani akan duk wani abu da ya shafi addini da kuma lamuran duniya, kebance Ahlul zikri a wannan Ayar yana nuna haramta tambayar wadanda ba ma’abota kwarewa a cikin sani ba.