Yi wa mutane izgilanci

Egypt's Dar Al-Ifta

Yi wa mutane izgilanci

Tambaya

Mene ne hukuncin yi wa mutane izgilanci ta hanyar “Comics”?

Amsa

Daukan mutane a hoto da yada bidiyoyin da hutunan ta hanyar izgilanci na “comics” haramun ne a shari’ar Musulunci, kuma dokoki ma sun hana; wannan haramci da hanin suna kara tsanani idan mutanen da aka dauka din an dauke su ne a yanayin da suke cikin matsaloli; musamman a irin yanayin da kamata ya yi al’umma ta hadu ta taimaka masu domin su fita daga cikin yanayi da kalubale masu wahala da suke fuskanta. Yin izgilanci ga wanda yake cikin matsala ba dabi’a ce ta Musulmi ba, ko kuma yi wanda ya tsaya tsayin daga domin warware matsalarsa izgilanci, ko kaskantar da shi, da rashin muhimmanta shi, ba tare da gabatar da masa da kowane irin kokari da zai taimaka masa wajen fita daga matsalar da yake ciki ba; lallai kowa yana da hakkin furta albarkacin bakinsa, amma fa hakan yana da ka’idoji da sharudda, a cikinsu akwai: rashin yin izgilanci da tozarta wasu, ko da ta hanyar hoto ko yin Magana ne, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Ya ku wadanda kuka yi imani, kada wasu mutane su yi wa wasu mutane izgilanci, ta yiwu sun fi su alhairi) [al- Hujrat: 11].

 

Share this:

Related Fatwas