Tasirin yada jita- jita a cikin al’umma
Tambaya
Mene ya wajaba Musulmi ya yi game da jita- jitan da ake yadawa?
Amsa
Yada labaran kuskure ko na karya, ko wadanda suke cutar da al’umma ta kafafen sadarwa na zamani da wasunsu haramune a shari’ar Musulunci, mai aikata haka kuma yana aikata manyan zunubai ne da aka haramta.
Lallai Allah Madaukakin Sarki ya wajabta wa Musulmai yin bincike da tabbatar da gaskiyar labarai kafin a gina kowane irin hukunci akansu, ya kuma bayar da umurnin mayar da komai zuwa ga masanansa kafin a yada shi, ko a yi Magana akansa; Allah mai girma ya ce: (Ya ku wadanda kuka yi imani, idan har wani fasiki ya zo maku da wani labara, to ku bincike, gudun kada ku cutar da wasu mutane ba tare da sani ba, ku zo kuna nadama akan abin da kuka aikata) [al- Hujrat: 6].
Mai girma da daukaka ya hana sauraron jita- jita da yada ta, ya kuma zargi wadanda suke yamadidi, da yada jita- jita da fitintunu, Allah Madaukakin ya ce: (Idan ma da sun fita jahadin tare da ku, da fitar tasu ba za ta kara maku karfi ba, hasali ma, za su kawo rudani ne a cikinku, ko su yi gaggawar kirkirar fitina, su kuma yada ta a tsakaninku, kuma a cikinku akwai wadanda suka jahilci mummunar niyyarsu, ta yiwu su yaudare su da maganganunsu, ko su saurari kiran da suke yi na fitina saboda raunin da suke da shi, lallai Allah yana da cikakkiyar masaniya da wadannan munafukan, wadanda suke cutar da kawunansu, da barnar da suka kulle a cikin zukatansu) [at- Tauba: 47].
Wannan kuwa ya faru ne saboda mummunan tasirin da haka yake a cikin addinin da mutunci da kayayyakin al’umma da yake yi, kai har ma da rayuwarsu.
Wanda ya kirkiri jita- jita, da wanda ya yadata, da wanda ya gasgata ba tare da bincike ba dukansu sun yi tarayya wajen aikata zunubi da aka haramta.