Sayen mota ta hanyar gabatar da tsohuwar mota da yin ciko a karbi sabuwa.
Tambaya
Shin ya halatta a sayi mota ta hanyar gabatar da tsohuwar mota da yin ciko a karbi sabuwa?
Amsa
Sayen mota a karkashin shirin gwamnati na bayar da makwafin motoci abu ne da ya halatta a shari’ar Musulunci; domin wannan sayen yana kunshe ne da sayar da tsohuwar mota, da sanya kudin ya zama wani kaso ne na sayen sabuwar motar da za a saya, wadda take da tallafi daga gwamnati, banki kuma yake shiga tsakanin mai sayar da sabuwar motar domin ya biya kudin sayen, wannan ba shi da wata dangantaka da riba; saboda idan akwai haja a tsakani, to babu batun riba.