Hukuncin fadin lafazin “Ubangijinmu ya tuna da shi”
Tambaya
Mene ne hukuncin wanda yake cewa idan wani ya mutu: Ubangijinmu ya tuna dashi?
Amsa
Wani abu da ya yadu a bakunan misirawa shine yanda suke fadin cewa: “Ubangijinmu ya tuna dashi” bayan sun tambayi mutum akace musu ya rasu, wanda hakan yake saurin zuwa kwakwalwan mai sauraro kan samuwar dalili dake nuna cewa hakika mutumin ya rasu ya koma zuwa ga Allah, a shari’ance hakan ba laifi bane, bai halasta a munana zato wurin daukar zancen a ma’anarsa na harshe ba, wanda shine danganta mantuwa ga Allah Ta’ala, - wanda hakan ya koru ga Allah Ta’ala – Amma abinda ya zama wajibi a fahimta anan shine ma’anar majazi wato wanda ba na zahiri ba, wato dai shine ya samu rahamar Allah, wannan zancen na misirawa ya kunshi fatansu mai kyau da samun rahama ga mamaci na fita daga kuncin duniya zuwa yalwar rahamar Allah bayan rasuwarsa da babu mai kuntata bayan samun rahamarsa, hakanan wannan zancen ya kunshi cewa ita mutuwa hutu ce ga mumini bayan shan wahalar duniya da tsananinta, dukkan wadannan ma’anoni masu kyau ne da wannan zancen na misirawa ya kunsa.