Ka’idojin sada zumunci

Egypt's Dar Al-Ifta

Ka’idojin sada zumunci

Tambaya

Mene ne ka’idojin sada zumunci?

Amsa

Allah mai girma da daukaka ya bayar da umurnin sadar da zumuni a cikin ayoyi masu yawa na Alkur’ani mai girma, abin da aka sani ne a cikin shari’a cewa ita sada zumunci tana bambanta daidai da bambancin zamunna da yanayi, daga mutum zuwa mutum, takan kasancewa ta hanyar da mutane suka saba na saduwa da juna, Kaman ziyar da sauran duka nau’o’in sada zumunci na zamani. Ingantaccen zance shi ne mazumunta su ne ‘yan uwan iyaye biyu. Wajibi ne mutum ya sadar da zumunci, ya kuma ba su hakkinsu koda kuwa su sun yanke shi, zai yi haka ne saboda ya samu lada daga Allah Madaukakin Sarki.

Share this:

Related Fatwas