Sayar da zinare da zurfa a biya a yayyanke
Tambaya
Mene ne hukuncin sayar da zinare da zurfa a biya a yayyanke tare da kari akan kudinsu na asali?
Amsa
Sayen zinare ko azurfa da aka sana’anta su, da sayar da su ta hanyar biyan kudinsu a rarrabe, da kudinsa duka, ko wani sashe nasa tare da karin da ya dace a kudin, da za zama makwafi ne na lokacin da aka yi ittafaki akansa a cikin yarjejeniyar cinikayyar, abu ne da shari’a ba ta hana ba; saboda ya halatta ya halatta a sayar da abu da kudi hannu nan take, da kuma jinkirta biyan kudi zuwa wani sanannen lokaci, da sanannen karin kudin da zai kwafe makwafin lokaci sannanen da aka saka, wannan abu ne da ya halatta a shari’a, saboda zinare da azurfa a yanzu sun zama haja kaman sauran hajoji, illar kasancewarsu kudi, da it ace take wajabta kamanceceniya, da sharadin cika shekara, da amsa a majalisar cinikayya sun kau.