Ma’anar kawama
Tambaya
Mene ne kawama “dankan nauyi”?
Amsa
Allah ya sanya alaka a tsakanin ma’aurata ta ginu ne akan kauna da tausayi a tsakaninsu, sai Allah Ta’ala ya ce: (Yana daga cikin ayoyinsa halitta muku mataye daga jikunanku domin ku samu natsuwa sannan ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku lallai a cikin haka akwai ayoyi na ni’ima ga mutanen da suke yin tunani)[Roum:21].
A wasu lokutan wadansu abubuwa suna faruwa da suke sanya iyali suke daukan wadansu matakai da suke amfanar dasu, don haka ne ma Allah ya baiwa namiji hakkin daukar mataki bayan shawartan matarsa da sauran dangi, to wannan shi ake kira da kawama, wanda aka ambata a cikin Kur’ani Maigirma, Allah Ta’ala ya ce: (suma mata suna da hakki akan mazajensu kwatankwacin hakkin da maza suke da shi akan matan na kyautatawa sannan maza suna da daukaka akan su matan)[Albakarah:228], hakanan fadin Allah Ta’ala: (Maza su ne masu tsayuwa akan mata da abin da Allah ya fifitasu dashi akan sashinsu da kuma abin da suka ciyar daga dukiyarsu)[An-nisa:34].
Abin da ake nufi da kawama: shi ne nauyin da namiji ke dauka na kulawa da matarsa da kuma iyalinsa ta wurin ciyarwa da kiyayewa da kulawa tare da biya musu bukatunsu na yau da kullum, ma’anar kawama bata nufin tilasci da kamakarya na ra’ayi, abin da ya kamata shi ne daukar mataki bayan shawartawar namiji ga matarsa ko iyalinsa da hakan zai taimaka wurin mashalarsa da iyalinsa, don haka sai mugane cewa kawama nauyi ne da Allah Madaukakin Sarki ya dorawa namiji.