Bayanin abin da ayar (Da a ce za su...

Egypt's Dar Al-Ifta

Bayanin abin da ayar (Da a ce za su mayar da shi zuwa ga Manzon Allah, da zuwa ga majibinta al’amurra a cikinsu, da masu istinbadin cikinsu sun san shi) [an- Nisa’i: 83] take nufi

Tambaya

Mene ne abin da ayar (Da a ce za su mayar da shi zuwa ga Manzon Allah, da zuwa ga majibinta al’amurra a cikinsu, da masu istinbadin cikinsu sun san shi) [an- Nisa’i: 83] take nufi?

Amsa

Allah Madaukakin Sarki yana cewa: (Da a ce za su mayar da shi zuwa ga Manzon Allah, da zuwa ga majibinta al’amurra a cikinsu, da masu istinbadin cikinsu sun san shi) [an- Nisa’i: 83], majibinta al’amurra su ne malamai da shugabanni.

Su malamai su ne ake komawa zuwa gare su wajen fahimtar hukunce- hukuncen shari’a da saukar da su akan ayyuka da maganganun mutane.

Su kuwa shugabanni: su ne suke dauke da alhakin tilastawa a zartar da hukunce- hukuncen a aikace, saboda a samar da maslahar al’umma, su ne kuma aka daura wa alhakin gudanar siyasar shari’a, da gyara bayi, Alkali Abubakar Bn Arabi a cikin littafin “Akhamul Kur’an” [1/472] ya ce: “Ingantacciyar Magana a wurina ita ce: su ne shugabanni da malamai a tare; su shugabanni saboda su ne asalin masu gudanar da al’amurra, su ne suke yi hukunci. Su kuwa malai: saboda wajibi ne a tambaye su, bin kuma fatawarsu shi ma wajibi ne”.

Share this:

Related Fatwas