Kwashe ruwa daga kan tituna saboda ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Kwashe ruwa daga kan tituna saboda saukan ruwan sama.

Tambaya

Mene ne ladan kwashe ruwan sama da ya kwarara akan hanyoyi da tituna?

Amsa

kwashe ruwan saman da ya kwarara a kan tituna da hanyoyi zuwa inda aka ware na musamman yana daga cikin kawar da cuta daga hanya, kuma hakan yana daga cikin ayyukan da ake son aikatawa a shari’ance, shi kawar da cuta daga kan hanyar da mutane suke wucewa yana daga cikin rukunin imani, an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara masa yarda ya ce: Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa  Alihi wa Sallam ya ce: (Shi imani yana da rukuni guda saba’in da wani abu, mafificin rukunin shi ne fadin la ilaha illallah, mafi kankantar rukunin shi ne kawar da cuta daga kan hanya, kunya rukuni ne daga cikin rukunan imani,) anyi ittifaki akan wannan Hadisin.

Shi mutum idan ya aikata aikin alheri irin haka zai samu lada mai yawa a duniya da lahira, an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara masa yarda, daga Annabi SallallaHu AlaiHi wa  Alihi wa Sallam ya ce: (Hakika naga wani mutum a cikin Aljanna yana ta kaiwa da komowa saboda wata bishiya da ya sareta daga kan hanya, wacce ta kasance tana cutar da mutane), a cikin wata ruwaya kuma ta daban ta Imam Bukhari a “Sahih” Manzon Allah  SallallaHu AlaiHi wa  Alihi wa Sallam ya ce: (A ya yin da wani mutum yake tafiya akan hanya sai yaga wani reshe na kaya akan hanya sai ya kawar da shi, sai Allah ya gode masa kan wannan aiki ya gafarta masa) Muslim.

Share this:

Related Fatwas