Kwadaitarwar da shari’a ta yi game da hadin kai
Tambaya
Ta yaya ta kwadaitar game
Amsa
Shari’a ta kwadaitar game da hadin kai, kuma Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya karfafa bayani game da muhimmancin hadin kai, da nesantar rarrabuwar kawuna; wajen samun taimakon Allah da dacewarsa, yana cewa: (Taimakon Allah yana tare da jama’a) [al- Tirmiziy da an- Nasa’i] daga ruwayar Ibn Abbas (Allah ya kara yarda da su.
Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam ya bayyana cewa hadin a kai ya fi rarrabuwar kawuna alhairi, haduwa ya fi sabani; yana cewa: (Idan kun ga sabani na rarrabuwa, to nah ore ku da bin inda jama’a mafi yawa suke) [Ibn Majah].