Son Ahlul Baiti da bayanin falalars...

Egypt's Dar Al-Ifta

Son Ahlul Baiti da bayanin falalarsa

Tambaya

Yaya shari'a ta kwadaitar game da son Ahlul Baiti, yana kuma falalar da yake cikin yin haka?

Amsa

Shari'ar Musulunci ta bayar da umurnin a so Ahlul Baiti, 'yan gidan Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam); Allah mai girma ya ce: (Ka fada masu cewa: ban a tambayarku wani lada game da sakon da nake isar maku, sai soyayya ga makusantana..) [as- Shura: 23], an ruwaito ingantaccen bayani daga Ibn Abbas (Allah ya kara yarda da su) game da tafsirin ayar, a abin da Imam al- Bukhari ya ruwaito a cikin "Sahih", ya ce: "Babu wani dangi daga cikin dangogin Kuraishawa face yana da makusanta a ciki; ya ce: kawai dai ku sada kusancin da yake tsakani da ku", wannan wasici ne da makusantansa (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), inda Allah mai girma ya umurce shi ya sanar da mutane.

Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya umurce mu da son iyalan gidansa, da riko da su, ya kuma yi masa wasici da su (Allah ya kara yarda da su) a Hadisai masu yawa, a cikinsu akwai wanda ya zo daga Abdullahi Bn Abbas (Allah ya kara yarda da su), ya ce: Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Ku so Allah saboda ni'imominsa da yake kwarara maku, ku kuma so ni saboda son Allah, ku kuma iyalan gidana saboda soyayyata) [al- Tirmiziy].

Share this:

Related Fatwas