Tara na kudi

Egypt's Dar Al-Ifta

Tara na kudi

Tambaya

Mene ne hukuncin cin tara na kudi?

Amsa

Ukuba ko tarar da kotu take daura wa mutumin da yake da taurin bashi, a matsayin rage wa wanda yake bin bashin asara, ba shi a cikin babin riba, hasali ma yin haka yana cikin kiyaye dukiyoyin mutane ne; gudun kada masu kwadayi da neman na banza, da mayaudara da makaryata su cinyeta, Hadisi ingantacce ya zo daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Duk wanda ya amshi kudin mutane (bashi) da niyyar biya, Allah sai ya ba shi ikon biya, wanda kuma ya amsa da niyya ya cinye, sai Allah ya hana shi ikon biya), haka ma al- Bukhari ya kawo daga Abuhuraira (Allah ya kara yarda da shi) cewa Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Taurin bashin mutumin da yake da shi, zai halatta a yi masa ukuba, a kuma ci mutuncinsa), taurin bashi shi ne mutum ya ki biyan hakkokin da suka rataya akansa, wannan nau’I ne cikin nau’o’in zalunci, wanda ya halatta alkali ya tsare shi, ya kuma yi masa ladabi da ukuba.

Share this:

Related Fatwas