Sake amfani da bola
Tambaya
Shin ya halatta a sake yin amfani kayayyakin bola da dagwalo?
Amsa
Sake juya kayayyakin bola daga yanayin da ba za a iya amfani da sub a, zuwa yanayin da dan Adam zai iya amfana da su, bayan an sauya hakikaninsu da sifofinsu, ya kuma zama babu najasa a cikin wannan abu: to lallai wannan abu ne da ya halatta a shari’ar Musulunci.