Taba Alkur’anin da aka rubuta shi d...

Egypt's Dar Al-Ifta

Taba Alkur’anin da aka rubuta shi da rubutun makafi ga mutumin da ba shi da tsarki

Tambaya

Mene ne hukuncin taba Alkur’anin da aka rubuta shi da rubutun makafi ga mutumin da ba shi da tsarki?

Amsa

Wajibi ne Musulmi ya girmama Alkur’ani mai girma, ya mutunta shi, ya kuma tsarkake shi, ya kuma ba shi kariya. A cikin nau’o’in girmama shi da kiyaye shi akwai kada wani ya taba shi sai mai tsarki, bai halatta wanda ba shi da tsarki ya taba shi ba, shin rashin tsarki da karamin hadasi ne ko babban hadasi, shi ma Alkur’ani da aka rubuta shi da bakaken Burayel na makafi yana daukan irin wannan hukuncin, wajibi ne a kiyaye shi a kuma mutunta shi, haramun ne wanda ba shi da tsarki ya taba shi, akan zababbiyar magana daga cikin maganganun malamai.

Wanda kuma hakan ya yi masa wahala, ko zai shiga cikin damuwa, yana kuma bukatar ya karanta Alkur’ani daga cikinsa kai- tsaye; saboda wata lalura, ko koyo, ko kuma wahalar samun abin da zai taimaka masa wajen yin tsarki, to zai iya yin amfani da shi a irin wannan yanayi; da haka an yi koyi da wanda ya halatta haka kenan a cikin malaman fikihun mazhabar malikiyya.

Share this:

Related Fatwas