Zuwa wurin bokaye da ‘yan tsubbu

Egypt's Dar Al-Ifta

Zuwa wurin bokaye da ‘yan tsubbu

Tambaya

Mene ne hukuncin zuwa wurin bokaye da ‘yan tsubbu?

 

Amsa

Shari’ar Musulunci ta hana zuwa ko komawa wurin bokaye da ‘yan tsubbu, da dogara da su wajen samun wani alhairi, ko tunkude wani sharri; an ruwaito Hadisi daga Imran Bn Hussain (Allah ya kara yarda da shi) cewa: Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Wanda ya yi shu’umanci wa kansa, ko ya yarda da shu’umanci da aka yi masa ba shi tare da mu, haka ma wanda ya yi wa kansa bokanci, ko ya yarda da bokancin da aka yi masa, ko ya yi tsafi, ko ya yarda da tsafin da aka yi masa, duk wanda ya je wurin boka, ya kuma gasgata shi a abin da ya fada, to kuwa ya kafirce wa abin da aka saukar wa Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) [al- Bazzar da isnadi Hasanun], haka ma Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya lissafa zuwa wurin wadannan mutane da gasgata su sun zama dalilai ne na rashin amsan aiki, ya ce: (Wanda duk ya je wurin dan duba ya tambaye game da wani abu, ya kuma gasgata shi ba za a amshi sallolin darare arba’in ba) [Muslim].

Share this:

Related Fatwas