Yin Hajji maimakon mamaci
Tambaya
Shin idan matar da ta yi wafati ta nuna kwadayin danta ya yi aikin Hajji a maimakonta tun kafin ta yi wafatin, shin hakan zai iya zama wasiyya?
Amsa
Muddin dai mamaciyar ba ta yi wasiyyar danta ya yi mata aikin hajji bayan ta yi wafati daga cikin dukiyarta karara ba, to kuwa babu wanda yake da daman ya cire kudin aikin Hajjin daga cikin dukiyarta kafin a raba ba, koda kuwa an riya cewa tana kwadayin a yi mata.