Yin limancin mace a sallah.
Tambaya
Mene ne hukuncin limancin mace ga mata a sallah?
Amsa
Ya halasta mace ta jagoranci ‘yan’uwanta mata a sallah, idan za ta limancesu sai ta tsaya a tsakiyarsu, amma kar ta shiga gabansu, idan kuma mace za ta limanci wata mace daya ne to matar ta tsaya a damanta, kamar dai yanda maza suke nasu.