Kokwanto akan yankewar niyyar azumi
Tambaya
Mene ne hukuncin azumin wanda yake kokwanton yankewar niyyar azumin tadawwa’i?
Amsa
Hakane, yana iya yiwuwa ga wanda ya dauki azumi na tadawwa’i ya zarce da azuminsa, matukar bai karya azumin da ci ko sha ko wani abu ba, kokwanton yankewar niyya ko fita daga niyyar azumin ba ya lalata azumin.