Ya ake gane nisabin zakkar kayan sayarwa?
Tambaya
Ya ake gane nisabin zakkar kayan sayarwa?
Amsa
Ana lissafin kudin zakkar kayan da ake sayarwa ne bayan an cire kudaden da aka yi wa hajar hidima da su, wato dai tsabar "uwar kudin da ake kasuwanci da shi"
An shardanta – kafin fitar da zakka- uwar kudin ya zama ya kai nisabi, (wato dai abinda ya yi daidai da giram 85 na zinare).
Za a iya takaita hakan a wannan lissafin mai zuwa:
Gwargwadon zakkar kayan kasuwanci = (kimar kayan daidai da yanda farashinsa yake a kasuwa+ kudaden da suke shigowa hannun dan kasuwan+bashin da ake son a biya+ basussukan da wasu ke bin mai bayar da zakkar) x (%2,5), (nisabin zakkar ana kirgawa ne da wata na kamariyya) ko (2,577) a tsarin zagayowar shekara na shamsiyya.
Lissafin kowani dan kasuwa daban ne da na wani, shin dan kasuwan, shin mai sayar da dila ne ko dai dai, farashin tsaka-tsaki kuma ga wanda yake sayar da dila da dai dai duka.
Hukumar bayar da fatawa ta kasar Masar ta na bayar da shawara da a rinka komawa wurin kwararrun masu lissafi domin sanin hakikanin uwar kudin da a ke juyawa.