Hujja ta shari’a da ta hankali da za ta sanya a fita daga ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da Boko Haram..)
Tambaya
Mene ne hujja ko dalili na shari’a da na hankali da zai sanya a fita daga ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da Boko Haram..)?
Amsa
Lallai haramun ne shiga cikin ƙungiyar ISIS, fita daga cikinta kuma wajibi ne na shari’a da na hankali; ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da Boko Haram..) ƙungiya ce ta ta’addanci da ta yi hannun – riga da karantarwar Musulunci, suna kashe Musulmai, su ma ana kashe su, a daidai lokacin da shugabanninsu suke jin daɗin rayuwarsu, suke kuma gudun mutuwa, saboda haka, mene ne hikima a cigaba da zama a cikinta, kuma wane sakamako ne yake cikinta banda asarar duniya da ta lahira.
Lallai babu wani abu da haramcinsa a wurin Allah ya fi girma sama da haramcin zubar da jini ba tare da haƙƙi ba, tabba sabubuwan da ISIS take aikatawa na kisa, da satar mutane, da halatta dukiyoyin mutane akan ɓarna, to wallahi shi ne keta hurumin Allah, shi ne toshe hanyar gaskiya da sunan addini, kuma ba ruwan addini da shi.
Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana cewa: (Laifin da ya fi kowane laifi girma shi ne: haɗa Allah da wani, da kashe rai), su kuma suna kashe Musulmai, ba sa bambance tsakanin maza da mata, babba da yaro, suna aikata ɓarna a bayan ƙasa saboda su samar wa kawunansu da tarkacen duniya mai ƙarewa, akan gurɓatattun fahimta, Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana cewa: (Duk wanda ya yi fito- na- fito da al’ummata, yana kai masu hari na kan- mai- uwa- da- wabi, ba ya shayin muminan cikinta, ba kuma ya cika alƙawarin da ya ɗauka, to ba ni ba shi).
Duk wanda yake cikin wannan ƙungiya na mashaya jinin al’umma ya taɓe, kuma ya yi asara, ya kuma halaka, zai mutu ne mutuwa irinta jahiliyya, saboda Hadisin Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da yake cewa: (Duk wanda aka kashe shi a ƙarƙashin makauniyar tuta, yana kira zuwa ga ta’assubanci, ko yana taimaka wa ta’assubanci, to an kasha shi ne kisa na jahiliyya).