Bambanci tsakanin Ta’addanci “yama-...

Egypt's Dar Al-Ifta

Bambanci tsakanin Ta’addanci “yama- ɗiɗi” da Jahadi

Tambaya

Mene ne bambanci tsakanin Ta’addanci “yama- ɗiɗi” da Jahadi?

Amsa

Ta’addanci “yama- ɗiɗi” shi ne: yaɗa tsoro da razani a cikin al’umma ta hanyar aikata ayyukan tashin hankali irinsu: kashe- kashe, ko yaɗa fahimtar kafirta Musulmai na ta’addanci, ko yaɗa jita- jita da samar da halin rashin tabbas, da rusa amincin da yake tsakanin gwamnatoci da al’umma, da nufin biyan buƙatun siyasa.

Ita kuwa kalmar “Jahadi” ta samo asali ne daga aiki tuƙuru, wanda ake yi cikin wahala, saboda haka akwai jahadin zuciya, akwai kuma jihadi da maƙiya saboda tunkuɗe sharrin da suke son yi wa bayi da ƙasashe, kare kai abu ne da yake tattare da halittar ɗan Adam, kowa ya san haka, a cikin Alƙur’ani mai girma Allah yana cewa: (Ya Annabi Muhammadu –SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam- ka yi jahadi da kafirai da munafukai, ka tsananta masu..) [al- Tauba: 73].

An ruwaito Hadisi daga Jabir (Allah ya ƙara yarda da shi) ya ce: Wasu mayaƙa sun dawo wurin Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), sai (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Lallai kun dawo -dawowa na alhairi- daga ƙaramin jahabi, za kuma ku shiga cikin babban jahadi.) sai suka ce: Mene ne babban jahadi? Sai ya ce: (Bawa ya yaƙi son zuciyarsa).

Jahadi suna ne na yaƙar azzalumi da tunkuɗe sharrinsa, wannan abu ne da ya halatta, sa’ilin da tashin hankali da lalata dukiyoyin al’umma da masu tsattsauran ra’ayi suke yi kuma shi ne ta’addanci da yama- ɗiɗi, koda kuwa sun yi ƙaryar cewa abin da suke yi jahadi ne, gaskiya yaƙarsu da hana su saƙat shi ne ainihin jahadi.

Share this:

Related Fatwas