Daidaito tsakanin mace da namiji

Egypt's Dar Al-Ifta

Daidaito tsakanin mace da namiji

Tambaya

Shin musulunci ya daidata namiji da mace?

Amsa

Alaka tsakanin namiji da mace alaka ce ta cike gurbi, wato kowa yana bukatar dan’uwansa, abin da yake bayyana na rashin ganin daidato a tsakanin maza da mata cikin wasu abubuwa ba ya nufin samun fifiko saboda banbancin halitta, hakan yana zuwa ne kawai domin ya nuna wasu dalilai da tushen wasu lamura da aka sanya, mafi muhimmancinsu anan shine bayyana banbancin nauyin da kowa cikinsu yake dauka, ko ya kebantu da shi, wanda hakan ya sanya rashin yiwuwar a iya daidaita maza da mata a komai, ya yin da shari’ar Musulunci ta bai wa namiji wani abu na matsayi wanda ba ta baiwa mace ba, to hakan ba ya nuna fifiko na halitta, sai dai kawai hakan wani wajibi ne da nauyi wanda aka dora masa domin mikewa da shi, domin ya rataya a wuyansa, amma hakan sam ba ya nuna fifikon namiji akan mace, haka nan wannan ba ya nuna wani tawaya daga cikin hakkokin mace.

Share this:

Related Fatwas