Hawarijawa su ne ƙungiyar da ta fi zama sharri a tarihin Musulunci
Tambaya
Mene ne ya sanya Hawarijawa suka su ne ƙungiyar da ta fi zama sharri a tarihin Musulunci?
Amsa
Bayyanar ƙungiyar Hawarijawa yana cikin manyan bala’o’in da suka faru da wannan al’ummar bayan wafatin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), su ne suka kafirta sahabban Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), suka halatta jininsu, suka sauya saɓani akan ra’ayi ya zama sanadiyyar halatta jini da cin mutunci, suka kuma zubar da jinin waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba, suka kafirta Musulmai masu kaɗaita Allah, kai har Imam Aliyu Bn Abuɗalib (Allah ya ƙara yarda da shi) sun kafirta, daga bisani kuma suka kashe shi, duk da cewa yana cikin “Hulafa’ur Rashidun”, wanda akansa ne Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yake cewa: (Kai ɗin nan a wurina kaman yanda Haruna yake a wurin Musa ne, kawai dai babu Annabi ne a bayana).
Hatsarin wannan ƙungiya yana ƙara bayyana ne ta hanyar irin yanda suke lulluɓe kawunansu da yawaita ibadar ƙiyamul- laili da azumi, wanda hakan yake ruɗar waɗanda ba su da zurfin tunani, ya sanya su zaci cewa lallai akan gaskiya suke, saboda haka ne ma Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya gargaɗe mu game da su. Ingantaccen Hadisi ya zo daga Aliyu Bn Abuɗalib (Allah ya ƙara yarda da shi), cewa lallai Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (A ƙarshen zamani wasu jama’a masu ƙarancin shekaru za su fito, waɗanda tunaninsu na wawacin ne, suna furta kalmomin fiyayyen halitta, suna kuma karanta Alƙur’ani, amma ba ya wuce maƙogwaronsu, suna fita daga addini kaman yanda kibiya take fita daga baka, idan kun haɗu da su ku kashe su, domin akwai lada a wurin Allah ranar alƙiyama ga wanda duk ya kashe su).