Sayar da magungunan da ba a san asalinsu ba.
Tambaya
Mene ne hukuncin sayar da magungunan da ba a san asalinsu ba, kuma hukuma ba ta bayar da izinin sayar da su ba?
Amsa
Irin yanda wasu masu shagunan sayar da magunguna suke harkar sayar da magungunan da ba a san asalinsu ba, kuma ma’aikatar lafiya ba ta bayar da izinin yaduwarsu ba abu ne da ya haramta a shari’ar Musulunci; lallai nassoshin shari’a sun zo da bayani akan hana cutar da rayuka, da jefa su cikin halaka, sun kuma bayar da umurni kiyaye su ga barin dukan hatsarurruka, Allah mai girma ya ce: (Kada ku jefa kawunanku cikin halaka) [al- Bakra: 195], babban malamin nan Ibn Ashur ya fada a cikin littafinsa “al- Tahrir wan Tanwir” (2/215) cewa: (Samun aikatau din “Tulquw” a cikin siyakin hani yana nuni ne zuwa ga hana kowane irin hali na jefa rayuwa cikin hala, ma’ana, duk wani dalili da zai kai zuwa ga halaka da gangan, to shari’a ta hana, kuma haramun ne, muddin ba wani dalili ne ya zo da zai sanya a cire wannan haramcin ba).
Haka ma yada su saba wa shugaba ne da Allah ya bayar da umurnin a yi masa biyayya, Allah mai girma ya ce: (Ya ku wadanda kuka yi imani, ku yi wa Allah biyayya, ku kuma yi wa Manzon Allah biyayya, da shugabannin cikinku..) [an- Nisa’i: 59]; lallai doka a kasar Misra ta haramta yada magungunan da ba a yi izinin yada sub a, shin masu yadawar masu sayar da magunguna ko waninsu ma’ana masu shiga tsakani, kaman yanda ya zo a doka mai lamba (28) na dokar aikin sayar da magunguna, mai lamba (127) ta shekarar 1955.