Hatsarin yin karatun addini ba a hukumomin da abin ya shafa ba, da kuma dogara da su a matsayin hanyoyin samun ilimi ba tare da komawa zuwa ga wata madogara ta addini ba.
Tambaya
Mene ne hatsarin yin karatun addini ba a hukumomin da abin ya shafa ba, da kuma dogara da su a matsayin hanyoyin samun ilimi ba tare da komawa zuwa ga wata madogara ta addini ba?
Amsa
Waada yake koyon ilimin Shari’a ta hanyar ya wayar da kansa ba a hukumomin addini, ba kuma tare da ya dogara da wata madogara ta ilimi ba hatsari ne babba akansa! Wannan hatsarin ba wai ya taƙaita akansa ne kawai ba, a’a ya ƙetara har zuwa gaba ɗayan al’umma, domin a mafi yawan lokaci, irin wannan mutumin yankan zaci cewa lallai ya yi karatu, hakan kuma ya sanya ya fara mu’amala da al’umma, yana mai ɗaukan kansa a matsayin malami masani ba kuma tare da ya cancanci ya zama hakan ba, wannan mu’amala zai zama mu’amala ce mai cutarwa, domin dai a haƙiƙa bai kai karanci komai ba, mafi kyawon sakamakon da irin wannan mutumin zai samu shi ne ya gane cewa bai sami nasara a yunƙurinsa na neman ilimi ba, himmarsa ta gaza, ya zama al’umma su yi asarar himmarsa da an yi amfani da ita ta nagartacciyar hanya, bugu da ƙari, kusan za a iya cewa kaso ɗari bisa ɗari na masu tsauraran ra’ayi da al’ummar Musulmai suke kokawa da su, dukansu ɗaliban ilimi ne da suka nemi ilimi ba a inda ya dace ba, sun nemi ilimi ba a kan wani sanannen manhaji ba, babu kuma wani sanadi da ake la’akari da shi, babu kuma shahada. Lallai karantar ilimin addini –a haƙiƙa- daidai yake da karantar sauran ilmomi, yana da sharuɗɗa da kayan aiki da kuma yanayi na musamman.