Bambancin da yake tsakanin hukuncin...

Egypt's Dar Al-Ifta

Bambancin da yake tsakanin hukuncin zato “al- Zanniyyat” da yankakken hukunci “al- Ƙaɗ’iyyat” a Musulunci

Tambaya

Mene ne bambancin da yake tsakanin hukuncin zato “al- Zanniyyat” da yankakken hukunci “al- Ƙaɗ’iyyat” a Musulunci? Kuma saboda mene ne sanya hukuncin zato a wurin yankakken hukunci ya zama ɗaya daga cikin dalilan samun tsattsauran ra’ayi da ta’addanci?

Amsa

Yankakkun hukunce- hukuncen Musulunci su ne waɗanda suke ɗauke da sifar Musulunci, waɗanda babu saɓani akansu, inda duka Musulmai na da da na yanzu, na gabas da na yamma, babba da yaro suka haɗu akansu, alal misali: Ka’aba ce alƙiblar yin sallah, da sallar Azuhur raka’a huɗu ne, da wajibi ne mace ta rife kanta da sauransu, saɓanin hukunce- hukunce na zato, waɗanda z aka samu akwai fahita biyu ko uku, kai akan ruwaito fahimta sama da goma sha takwas akan mas’ala guda ɗaya daga malami mujtahidi guda ɗaya. Wannan saɓanin yana ɗauko tsarin rayuwar Musulmai ne, wasunsu suna aiki da fahimta kaza, wasunsu kuma suna aiki da fahimta kaza, daidai da rinjayarwa, ko kuma fatawar malaman garinsu, ko na zamaninsu. Babban kuskuren da yake kai wa zuwa ga tsattsauran ra’ayi shi ne ƙuntata wa Musulmai, da ɗaukan hukuncin zato a mayar da shi yankakken hukunci da aka haɗu akansa, da zaɓa magana ɗaya cikin waɗannan maganganun, tare da inkari wa duk wanda ya ɗauki magana ta biyu, kai ka shi shi ma yana cikin Musulunci ba ne! Lallai manyan malamai sun bayyana cewa: ba a yin inkari akan mas’alar da akwai saɓani akanta. 

Share this:

Related Fatwas