Ingantacciyar fahimta dangane da yin hukunci da shari’ar Musulunci.
Tambaya
Mene ne ingantacciyar fahimta dangane da yin hukunci da shari’ar Musulunci, ta yaya masu tsattsauran ra’ayi suka yi yawo da hankalin mutane dangane hakan..?
Amsa
Ingantacciyar fahimta dangane da neman yin hukunci da shari’ar Musulunci shi ne “zartar da hukunce hukunce tare da komawa zuwa ga abin da shari’ar ta tanadar kan kowani lamari”; domin hukun-hukuncen Allah Mai girma da daukaka shi ne ya saukar da su, sai dai masu tsattsauran ra’ayi sun sauya wannan ma’ana, domin kuwa sun fahimci nassosin Al’kur’ani da Hadisai a bisa kuskure, inda suka kirkiro da wani sabon manhaji da aka gina shi kan kuskure, sannan suka sanya wannan manhajin nasu a matsayin shi ne shari’ar Musulunci, duk wanda ya ki aminta da wannan manhajin nasu to – a wurinsu – yana kin shari’ar Musulunci kenan, don haka ya zama mai mika wuya ga dagutu, haka nan suna kallon zartar da manhajinsu wurin shari’a shi ne na gaskiya wanda imani ba ya inganta idan mutum bai yi imani da shi ba, domin in ba haka ba, duk wanda ya bijirewa manhajin wurin zartar da shari’a to ya kafircewa Allah Mai girma da daukaka. A zahirin gaskiya hukunce hukunce na shari’a akwai wanda aka samu fahimtar juna akai tsakanin malamai na baya da na yanzu, tun daga gabashi har zuwa yammaci, wannan shi ne aka fi sani da madogaran shari’ar Musulunci, haka nan akwai wanda kuma aka samu sabani a kai, yin aiki da wani zance cikin zantuttukan malamai da suka samu sabani a junansu akansu yana daga cikin tsari na shari’a wanda yin hakan ba ya fitar da mutum daga kan tafarki, sannan rashin yin aiki da hukunce hukuncen Allah sabo ne ba wai lamari ne wanda yake fitar da mutane daga Musulunci ba, wannan shi ne abin da malamai masana fikihu suka tabbatar.