Cakuɗa ma’anoni ɗaya ne daga cikin ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Cakuɗa ma’anoni ɗaya ne daga cikin manyan bala’o’in da suke faɗa wa al’umma

Tambaya

Mene ne ya sanya cakuɗa ma’anoni ɗaya ne daga cikin manyan bala’o’in da suke faɗa wa al’umma? Kuma mene ne misalin haka daga rayuwar al’umma? Yaya tasirin haka wajen yaɗuwar tsaurin ra’ayi da ta’addanci?

Amsa

Lalacewar ma’anoni, da cakuɗa su ɗaya ne daga cikin muhimman dalilai na yaɗuwar tsaurin ra’ayi da ta’addanci, sau da yawa masu tsattsauran ra’ayi suka  kafa hujja karkatattun akan ayyukansu da wasu ma’anonin na kuskure kuma gurɓatattu da suka danganta wa Alƙur’ani ko Hadisai, kaman irin yanda suka fahimci maganar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da yake cewa: (Umirtu an uƙátilan nasa hatta yashhadu allá Ilaha illalLah…) [al- Bukhari da Muslim], inda daga wannan Hadisin suke fahimtar cewa: an umurci Musulmai ne da su yaƙi waɗanda ba Musulmai ba har sai sun shiga Musulunci!.. Wannan gurɓatacciyar fahimta ce, babu wani daga cikin jagororin Musulmai da ya faɗi haka, ko ya fahimci haka, wannan fahimta tasu ta kai zuwa ga babban hatsari da bala’i, mafi ƙarancin wannan bala’in shi ne gwama addinin tausayi da jinƙai da wata lalatacciyar sura a cikin zukatan mutane, magana ta gaskiya wannan magana ta Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da yake cewa: (Umirtu..) ta shi ce shi kaɗai, bai shafi waninsa ba, haka ma kalmar (uƙátilu) tana nuni ne zuwa da ayyukan ɓangarori biyu, ɓangaren farko na wanda ya fara yaƙi, an kuma sami lokaci mai tsawo kusan shekara goma sha uku kafin a bayar da umurnin mayar da martani, kalmar (Annasa..) tana nufin mutanen da suke yaƙar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) cikin mushrikan Ƙuraishawa da wasunsu, wannan gama – garin lafazi ne, amma keɓantacciyar ma’ana ake nufi.

Share this:

Related Fatwas