Ware wani kaso na zakka domin taimakon wadanda ake bi bashi da yi wa al’umma hidima.
Tambaya
Mene ne hukuncin ware wani kaso na zakka domin taimakon wadanda ake bi bashi da yi wa al’umma hidima?
Amsa
Ya halatta a ware wani kaso daga cikin kudin zakka saboda taimaka wa wadanda ake bi bashi, da kuma bayar da gudummuwa wajen kyautata ilimantarwa, da gabatar da wasu ayyuka na kasuwanci da za su habaka dukiya, da sharadin ya zamana maslahar talakawa ne ya sanya aka yi haka, bai wa talakawa da mabukata abubuwan da suke matukar bukata na tufafi da abinci da wajen zama, da abubuwan rayuwa da karatu da lafiya da sauran al’amurran rayuwa, su ne abubuwan da wajibi ne a muhimmanta su a fara gabatar da su akan komai, domin zartar da babbar manufar shar’anta zakka da hikimarta, wadda Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yi nuni zuwa gare ta a inda yake cewa: (Za a karba daga hannun mawadatan cikinsu, a rarraba wa matalautan cikinsu).