Misalai guda hudu na mu’amalar Musulmi tare da mutanen da suke kusa da shi.
Tambaya
Menene misalai guda hudu na mu’amalar Musulmi tare da mutanen da suke kusa da shi.
Amsa
Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya bar mana wadansu misalai guda hudu da muke koya ta hanyar sirarsa mai girma, wato wasu halaye ne guda hudu da Musulmi zai yi mu’amala da wadanda suke kusa da shi, misali na farko shi ne: Misali na farko: Zaman Makkah; Inda Musulmi yake rayuwa a cikin wani yanayi da ake yakarsa ake yakar addininsa, amma duk da haka mun ga yanda Musulmi ya yi ta hakuri da cutarwar da ake masa, kuma yake rayuwa a cikin wannan yanayin. Misali na biyu: Misalin Zaman Habasha; Inda Musulmai suka rayu a garin da mutanen garin ba sa yakar Musulunci duk da cewa ba sa bin addinin na Musulunci, amma a cikin garin Musulmi na tarayya da waninsa a komai ya ba shi kulawa da girmamawa. Misali na uku: Zaman Madina; A farkon lamari, Musulmi ya rayu a cikin garin yayin da akwai mabiya addinai daban daban da kungiyoyi daban daban da kuma kabilu daban daban, don haka yanayin zamantakewa a wannan lokacin yana bukatar jan mutane a jiki da taimakekeniya da sauran mutane. Misali na hudu: Zaman Madina; A karshen lamari, inda garin ya kasance cike yake da Musulmai, mafi yawan mazauna garin Musulmai ne, ko a ce dukkan mazauna garin Musulmai ne, to matsayin Musulmai a wannan yanayi shi ne yin adalci da wayar da kai kafin kokarin yin hukunci. Saboda haka rayuwar Musulmi a kasarsa, ko a kasar wasu ba ta wuce wadannan abubuwa guda hudu da aka ambata a baya.