Hadiyyar ladan sadaka ga iyayen da ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Hadiyyar ladan sadaka ga iyayen da suka rasu.

Tambaya

Mene ne hukuncin bayar da ladan sadaka ga iyaye bayan wafatinsu?

Amsa

Amsa:

Allah mai girma ya wajabta yi wa iyaye biyayya, da kyautata masu a wurare masu yawa, Allah mai girma ya ce: (Lallai Ubangijinka ya riga ya hukunta kada a bauta wa kowa sai shi, sannan kuma iyaye a yi masu cikakkiyar biyayya, idan iyayen guda biyu, ko daya daga cikinsu ya kai matakin rauni, yana matakin gangara a cikin rayuwa, kada ka soma ka nuna kosawa, da rashin hakuri da abubuwan da suke yi, ta hanyar daga masu murya, kada kuma ka kyare su, kamata ya yi ka fada masu magana mai kyau da take cike da tausasawa, da kyautatawa, da kuma karramawa a gare su. Ka kwantar masu da kanka kasa, ka kankantar da kai a gare su, ka tausaya masu matuka, game da duk abin da ya shafe su ka rinka addu’a ka ce: Ya Ubangiji, ka tausaya masu, kaman yanda suka tausaya mini lokacin da suka raine ni ina karami) [al- Isra'i: 23- 24].

Saboda haka a cikin yi wa iyaye akwai: ka yi sadaka da sunansu ka sadaukar da ladan sadakar a gare su, musamman ma idan sadakar sadaka ce mai gudana da take cigaba da wanzuwa, lallai ladan zai sadu da su; Imam al- Bukhari ya ruwaito Hadisi daga Abdullahi Bn Abbas (Allah ya kara yarda da su) cewa: wani mutum ya ce wa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam): Lallai mahaifiyata ta rasu, shin idan na yi sadaka da sunanta za ta amfaneta? Sai ya ce: (Kwarai kuwa), sai ya ce:  to kuwa lallai ina da gonar dabino, ka zama shaida na yi sadaka da ita da sunanta.

 

Share this:

Related Fatwas